Rashin tabbas a Afirka: Dangote zai bude sabon ofis a Amurka

Rashin tabbas a Afirka: Dangote zai bude sabon ofis a Amurka

Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya ce zai bude sabuwar ofishi a birnin New York na Amurka domin ya rararraba hannun jarinsa don kaucewa hauhawa da sakan naira a Najeriya.

Da ake hira da shi a wani shiri mai suna Rubenstein Show a Bloomberg TV, Dangote ya ce, "Ka san cewa a Afirka muna da matsalar rage darajar kudadenmu, saboda haka muna son mu adana wasu daga cikin dukiyar mu."

Dama attajirin na Afirka kuma mutum mafi arziki a duniya na 95 yana da ofishi a birnin London.

Duk da cewa yana da kamfanoni biyar, a halin yanzu ba a san ko wane cikinsu zai bude mata reshe a New York ba.

Attajirin mai dan shekara 63 ya samu karin arziki na biliyan 4.3 a 2019 sakamakon saka jarin da ya yi a samar da siminti, flawa da sukari. Da zarar an kammala matatan man fetur din da ya ke ginawa wa arzikinsa zai kara bunkasa.

DUBA WANNAN: Albashi na duk wata N54 ne a matsayin malamin makaranta - Sanata Wamakko

Ana sa ran matatar zai rika samar da gangan man fetur 650,000 a duk rana.

Matatar man zai wadatar da 'yan Najeriya baki daya duba da cewa a yanzu kasar tana shigo da tattacen man fetur ne daga kasashen waje domin biyan bukatunsu.

Dangote kuma yana gina masana'antar sarrafa takin zamani a wurin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel