Iran ce ta baro jirgin saman Ukrainiyar da yayi hadari jiya - Amurka

Iran ce ta baro jirgin saman Ukrainiyar da yayi hadari jiya - Amurka

Cikin kuskure Kasar Iran ta baro jirgin saman Ukraniyar da yayi hadari ranar Laraba, inda dukkan mutanen ciki 176 gaba daya suka hallaka, jami'an kasar Amurka sun tabbatar.

Jirgin ya yi hadari ne bayan tashi daga filin jirgin saman Tehran.

Wannan hadari ya faru ne bayan kasar Iran ta kai hari sansanin Sojin Amurka biyu a kasar Iraqi.

Tashar CBS ta ruwaito cewa hukumomin leken asirin kasar Amurka sun yi ikirarin cewa sun ga rokoki masu inzami biyu gab da jirgin ya kama da wuta.

DUBA NAN Hukumar Hizbah ta kashe auren dole 330 da akayi a jihar Jigawa

Wata majiya ta bayyana cewa "Da alamun an ga karafunan roka mai linzami kusa da inda jirgin ya fadi."

Martani kan hakan, hukumar jiragen saman Iran ta ce rahoton Amurka karya ne.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce shi ga bai yarda da hadarin jirgin nan ba.

Trump ya ce jirgin ta tashi a wannan lokacin kuma akwai yiwuwan wani yayi kuskure

"Ni fa na san ruwa bai tsami banza. Ban san fadi saboda wasu na nasu zarge-zargen."

A ranar Laraba, Wani jirgin saman kasar Ukraine ya yi hatsari a Iran.

Dukkan fasinjoji 186 tare da matukan jirgin farar hular sun rasa rayukansu, kamar yadda Red Crescent na kasar Iran suka sanar.

Faduwar jirgin ya auku ne sa'o'i kadan bayan da Iran ta kai hari ga rundunar sojin Amurka don mayar da martani a kan kisan kwamanda Soleimani da Amurka tayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel