Da duminsa: Buhari ya watsawa Ministan lantarki kasa a ido, ya dawo da wanda ya dakatar

Da duminsa: Buhari ya watsawa Ministan lantarki kasa a ido, ya dawo da wanda ya dakatar

Shugaba Muhammadu Buhari ya soke umurnin dakatad da Marilyn Amobi a matsayin shugabar kamfanin sayar da wutan lantarkin Najeriya NBET.

Wannan na kunshe cikin wasikar da ya bayyana daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Bugu da kari, an dauke ma'aikatar daga ma'aikatar wutan lantarki zuwa ma'aikatar kudi.

Za ku tuna cewa a Disamban 2019, ministan wutan lantarki, Saleh Mamman, ya sallami Marylin Amobi, domin kawo gyara kamfanin.

Hakazalika ministan ya bada umurnin kafa kwamitin mutane biyar domin duba zarge-zargen da ake yiwa matar.

A bangare guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawar sirri da shuwagabannin kungiyar Malaman jami’a, watau ASUU, inda ake sa ran tattaunawarsu za ta tattara ne game da batun sabon tsarin biyan albashi na bai daya, watau IPPIS.

Idan za’a tuna, ASUU sun yi fatali da wannan sabon tsarin biyan albashi, inda suka bayyana cewa tsarin zai gurgunta ayyukan malamai a jami’o’in Najeriya tare da kawo tsaiko ga tsarin koya da koyarwa.

Bayan akawun gwamnatin tarayya ya yi barazanar hanasu albashi idan basu yi rijista ba, malaman jami'an sun lashi takobin tafiya yajin aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel