Najeriya zata samu cigaban tattalin arziki a 2020 - Bankin Duniya

Najeriya zata samu cigaban tattalin arziki a 2020 - Bankin Duniya

Bankin duniya yayi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai samu cigaba da kashi 2.1 a 2020, ya kara da cewa cigaban tattalin arzikin har da kungiyar tattalin arziki ta Afirka ta Yamma zai daidaitu da kashi 6.4.

Bankin duniyar ya sanar da wannan hasashen ne a wallafarsa ta tattalin arziki na duniya da ta saki a watan Janairu na 2020 wanda ya fita a ranar Laraba, kamar yadda jaridar The Punch ta ruuwaito.

Tattalin arzikin Najeriya zai samu cigaba da kashi 2.1 a 2021 da 2023, cewar bankin.

Tattalin arzikin Najeriya matsakaici bashi da tabbaci, cewar bankin a rahoton. Ya jaddada cewa tattalin arzikin Najeriya na kunshe ne da tsaiko ta fannin musaya da kuma hauhawar kaya.

Mataimakin shugaban bankin duniyar, Ceyla Parzarbasioglu, ya hori masu tabbatar da tsare-tsare a Najeriya da sauran kasashe masu tasowa da su rungumi tsare-tsaren gyaran da zai habaka tattalin arzikinsu.

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda fasto ke amfani da kwallon kafa don cire aljannu

"Matakan habaka yanayin kasuwanci, dokoki, tsarin bashi da kuma kokarin cigaba zai taimaka wajen tabbatar da habakar tattalin arzikin," ya kara da cewa.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, an samu raguwar hatsari ta fuskar kasuwanci, duk da kuwa an samu cigaban sanya hannayen jari da siye da siyarwa daga nakasar da suka samu a 2019.

Cigaba a tattalin arzikin kasar zai kai kololuwa har zuwa kashi 2.9, bankin ya kara da cewa.

Amma kuma, wannam cigaban zai dogara ne ga cigaban karfin guiwar masu zuba hannayen jari a wasu manyan bangarori na kasuwancin kasar nan, cigaba a bangaren samar da man fetur da kuma habaka a bangaren fitar da kayan gona zuwa kasashen ketare.

Bankin ya kara yin hasashe da cewa, za a samu nakasa a fannin tattalin azrki da kashi 1.4 a manyan kasashe a 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel