Yan bindiga sun kai hari makaranta a Kaduna, sun sace dalibai 4

Yan bindiga sun kai hari makaranta a Kaduna, sun sace dalibai 4

Wasu yan bindiga a ranar Laraba sun kai hari makarantar katolika dake garin Kakau, hanyar Abuja zuwa Kaduna kuma sun yi awon gaba da dalibai hudu.

Rahoton jaridar Vanguard ya ruwaito shugaban makarantar, Joel Usman, da cewa harin ya faru ne misalin karfe 10:30 da 11 na daren Laraba.

Yace: " Wasu yan bindiga sun kawo hari makarantar Good Shepherd Major Seminary jiya 8 ga watan Junairu, 2020 tsakanin karfe 10:30 zuwa 11 na dare."

"Bayan kirga dalibai da jami'an tsaro, mun nemi dalibai hudu mun rasa."

Amma har yanzu hukumar yan sanda basu saki jawabi kan lamarin ba.

A wani labarin mai alaka, Gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a garin Beni dake cikin karamar hukumar Munya na jahar Neja, inda suka yi awon gaba da babban limamin Masallacin Juma’an garin, Malam Umar Muhammad.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito baya ga babban limami Malam Umar, yan bindigan sun tasa keyar wasu mutane 20 da suka tilasta musu tafiya dasu daga garin Beni.

KUKARANTA: Buhari ya watsawa Ministan lantarki kasa a ido, ya dawo da wanda ya dakatar

Rahotanni da dama sun bayyana cewa yan bindigan da yawansu ya kai 50 sun yi ta shiga kauyuka daban daban ne suna yi ma jama’a fashi, tare da kwashe shanunsu, daga nan suka afka Beni da Kudami na karamar hukumar Paikoro, a ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel