Tsananin talauci yasa an daure wata mata bayan ta saci akuya ta sayar ta siyawa danta magani

Tsananin talauci yasa an daure wata mata bayan ta saci akuya ta sayar ta siyawa danta magani

- Wata kotun majistare dake zama a Osogbo ta yankewa wata mata mai suna Sadiat Jimoh hukuncin watanni 6 a gidan gyaran hali

- Bayan bincike da aka gudanar tare da sauraron shari’ar, an gano Sadiat ta saci akuya wacce zata kai darajar N45,000

- Wacce aka yankewa hukuncin ta bayyana cewa, ta yi hakan ne don ta siyar da akuyar don magance ciwon da danta yake fama dashi

Wata kotun majistare dake Osogbo ta yankewa wata mata mai suna Sadiat Jimoh hukuncin watanni 6 a gidan gyaran hali. Matar mai shekaru 30 a duniya ta samu wannan hukuncin ne bayan da aka kamata da laifin satar akuya mai kimanin kudi N45,000.

An gano cewa wacce aka yankewa hukuncin ta saci macen akuya ne daga wata Fausat Adegboga a ranar lahadi, 5 ga watan Janairu a yankin Agunbelewo na birnin Osogbo.

A yayin gabatar da shari’ar a gaban kotu, dan sanda mai kara wanda ya bayyana sunanshi da Abiodun Fagboyinbo ya sanar da kotun cewa “Sadiat Jimoh da wata mutum daya sun hada kai inda suka sace akuya a yankin Agunbelewo dake Osogbo a ranar 5 ga watan janairu.”

Fagboyinbo ya kara da cewa, wannan laifin kuwa yaci karo da wasu sassa na dokokin Criminal Code kuma abun hukuntawa ne a dokokin jihar Osun na 2002.

KU KARANTA: Barayi sun saci kaya na makudan kudade a shagon jaruma Samira Saje

An gurfanar da wacce ake zargin a ranar Talata, 7 ga watan Janairu, amma ta musanta zargin laifukan biyu da aka mata.

Ta kara da bayyana wa kotun cewa tana son amfani da kudin akuyar satan ne don magance ciwon da danta yake fama da shi.

A yayin mayar da martani a kan aukuwar lamarin, lauyan wacce ake kara, Abimbola Ige ya roki kotun da ta ji kan wacce yake karewa.

Kotun ta yanke hukuncin cewa za a daure wacce ake zargin na watanni shida tare da tarar N15,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel