Iran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba muddin ina shugaban ƙasa - Trump

Iran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba muddin ina shugaban ƙasa - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai taba bari kasar Iran ta mallaki makamin nukiliya ba muddin yana kan karagar mulki duk da ya nuna ba allamun ba zai sake kai mata harin soja ba bayan harin makami mai linzami da ta kai a sansanin Amurka a daren ranar Talata.

A daren ranar Talata, Iran ta harba makamai masu linzami fiye da 24 a sansanin Ayn al Asad da Erbil a Iraqi inda dakarun sojojin Amurka ke zaune a matsayin daukan fansa kan harin da Amurka ta kai da jirgi mara matuki da ya kashe babban kwamandan Iran Qassem Soleimani a ranar Juma'a.

Dakarun tsaro na musamman na Iran (IRGC) sun gargadi Amurka da ƙawayenta cewa za su kai harin daukan fansa cikin wata sanarwar da wani kafar yadda labarai na ƙasar IRNA ya fitar a ranar Laraba.

Sai dai a safiyar Laraba yayin wani taron manema labarai Trump ya ce babu wani baamurke da ya rasa ransa sakamakon harin da Iran ta kai kuma a shirye ya ke ya yi sulhu da Iran idan tana bukatar zaman lafiya na yaƙi ba.

Trump ɗin ya ƙara da cewa sai ƙaƙaba wa Iran ɗin takunkumin kasuwanci ne inda ya bukaci kasashen Turai da kungiyar NATO su mara masa baya wurin tsawatawa Iran inda ya ce yana da gangariyar makamai da zai iya amfani da su idan buƙatar hakan ya taso.

DUBA WANNAN: Jonathan ya yi karin haske kan batun sake takarar shugaban kasa a 2023

Ya ce, "Iran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba muddin ina shugaban kasa. Da fatan kowa ya tashi lafiya. Babu baamurke da ya mutu sakamakon harin da Iran ta kai a daren jiya."

Ya ƙara da cewa, "Bisa ga allamu Iran ba yaƙi ta ke so ba wanda hakan abu ne mai kyau ga kowa"

"Za mu ƙara saka wa Iran takunkumin kasuwanci har sai ta canja halin ta"

"Ya zama dole mu cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya tsakanin mu da Iran," inji Trump.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel