Kisar Qassem Soleimani: Wannan lamarin Amirka ne ba na Izra'ela ba - Netanyahu ya yi gargadi

Kisar Qassem Soleimani: Wannan lamarin Amirka ne ba na Izra'ela ba - Netanyahu ya yi gargadi

Firam Ministan kasar Israeela, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa rikicin dake faruwa tsakanin Amirka da Iran ya shafi jihohon Amirka ne kadai.

Benjamin Netanyahu ya gargadi hukumomin Israeli da karsu tsoma baki a rikicin dake gudana tsakanin kasashen.

Yayi gargadin ne bayan wani harin da gwamnatin kasar Iran ta kaiwa sojin kasar Amirka a Iraq.

Netanyahu yayin tattaunawa da jami’an tsaro ya bayyana cewa Israeli bata da hannu wurin kisan babban kwamandan kasar Iran, Qassem Soleimani.

Rahotanni daga Daily Mail sun nuna cewa Shugaban kasar Israela ya yabawa Shugaban kasar Amirka Donald Trump akan matakin da kasar ta dauka bayan harin da Iran ta kaiwa offishin jakadancin kasar Amirka dake Iraqi.

Duk da haka, a ranar talata, 7 ga watan janairu, Netanyahu, ya gargadi dukkan ministocin Israela dasu guji fitowa a kafofin watsa labarai dan tsokaci akan rikicin dake gudana tsakanin kasar Amirka da Iran.

Legit.ng ta rahoto cewa bayan kisar da kasar Amirka ta yiwa soleimani, Kasar Iran ta dauki fansar kai hari ga gidan soji biyu na kasar Amirka a ranar talata.

Gwamnatin kasar Iran tayi ikirarin cewa akalla yan Amirka 80 ne suka rasa rayukansu amma shugaban Amurka yace babu dan Amurkan da ya mutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel