Ba zamu sake kaiwa Iran hari ba amma zamu sanya takunkumi - Trump

Ba zamu sake kaiwa Iran hari ba amma zamu sanya takunkumi - Trump

Shugaban kasan Amurka, Donald Trump, ya yi jawabi ga al'ummar kasarsa kan harin da kasar Iran ta kai sansanin Sojin Amurka dake kasar Iraqi.

Trump a jawabinsa bai ambaci wani shirin kara kaiwa Iran wani sabon harin ba sabanin barazanar da yayi a baya.

Amma ya ce Amurka za ta kakabawa Iran takunkumin tattalin arziki har sai ta canza halayenta.

Ya ce gwamnatinsa a shirye take da hada kai da Iran wajen kawo cigaba duniya kamar yadda suka hada kai wajen yakar kungiyar ISIS.

"Ragargazan ISIS abine mai muhimmanci ga Iran kuma zamu iya aiki tare kan wasu abubuwa masu muhimmanci,"

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce babu dan Amurkan da ya samu rauni a harin bama-bamai masu linzamin da Iran ta kai sansanin Sojin Amurka dake Iraqi ranar Laraba.

Trump ya sanar da hakan ne a jawabin da yayi ga kasar a fadar White House.

Yace: "Mutan Amurka su godewa Allah kuma suyi farin cikin cewa babu dan Amurkan da harin daren jiya da Iran ta kai ya shafa."

"Babu wanda ya jikkata, dukkan Sojojinmu na nan cikin koshin lafiya, kuma abubuwa kadan aka lalata a sansanin Sojinmu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel