Rikicin cikin gida: PDP ta dare gida biyu a jihar Kano

Rikicin cikin gida: PDP ta dare gida biyu a jihar Kano

Jam'iyyar PDP reshen jihar kano ta sallami kwamitin shugabanninta na rikon kwarya, kuma ta nada kwamitin wasu mutane uku don jibantar lamarin jam'iyyar a jihar, kamar yadda umarni daga hedkwatar jam'iyyar na kasa ya nuna.

Shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Dala, Mahammina Bako-Lamido, ya sanar da manema labarai bukatar hedkwatar jam'iyyar na sauke shugabannin shine a sashin na 24 sakin layi na biyu da kuma uku, na kundin tsarin jam'iyyar da aka gyara a 2017.

Kamar yadda yace, kwamitin rikon kwaryar yayi aiki ne a cikin watanni uku.

Yace wannan cigaban ya biyo bayan wasikar da ciyamomin kananen hukumomi na jihar suka rubuta ga hedkwatar jam'iyyar tare da sanar dasu lokacin da za a sauke masu rikon kwaryar

"An rubuta wannan wasikar ne a ranar 21 ga watan Yuni 2019 kuma an rubuta wata ta tunatarwa ne a ranar 21 ga watan Augusta. Wasikar mai take 'korafi kan cin zarafi,' ta kai ga hedkwatar ne a ranar 12 ga watan DIsamba.

"An gon cewa, dukkan wadanda aka tura wasikar gabansu sun tabbatar da isarta amma babu wasikar mayar da martani har yanzu.

"A don haka ne, muka gane cewa majalisar kasar nan ta PDP da gangan taki saka baki a wannan lamarin tare da bada umarnin a nada sabon kwamiti don yin zabe a jihar Kano." in ji shi.

Bako-Lamido ya ce, saka baki daga babbar hedkwatar ta kasa zai shawo kan lamurran dake faruwa a kwamitin na ba bisa ka'ida ba. Ta hanyar haka ne za a iya kawo hadin kai tare da korar duk wata matsala ta PDP a jihar.

Ya ja kunnen 'yan jam'iyyar da su guji bayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar a jihar don biyayya ga kundin tsarin mulkin jam'iyyar a jihar.

A lokacin da aka tuntubi shugaban kwamitin rikon kwaryar, Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi, ya ce fusatattun 'yan jami'iiayar sun je kotu har sau hudu amma su ke cin nasara a duk hukuncin alkalin.

"Ba mu muka zabi kanmu ba. An nada mu ne kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanadar kuma ba a bamu wa'adi ba."

Ya ce, kwamitin masu rikon kwaryar zai cigaba da mulki ne har sai anyi taro kuma an umarcesu da su dena bayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel