Kisan Janar Sulaiman: Trump ya bayyana burinsa na ganin ya sasanta da kasar Iran
Biyo bayan kisan da Amurka ta yi ma babban kwamandan Sojan Iran, Janar Qassem Sulaiman, shugaban kasar Amurka, Donald J Trump ya sanar ma duniya manufarsa na ganin ya sasanta da gwamnatin kasar Iran.
Trump ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi ga al’ummar kasar Amurka, inda yace alamu sun nuna kasar Iran ta tsagaita, kuma ta dauki darasi duk kuwa da cewa ta kai harin makami mai linzami a wani sansanin Amurka dake kasar Iraqi.
KU KARANTA: Jami’ar BUK ta karrama wata Baturiya da ta kwashe shekaru 50 tana koyar da harshen Hausa
Sai dai Trump yace babu wani Sojan Amurka ko na Iraqi da ya mutu a sanadiyyar harin da Iran da kai, don haka ya yi kira ga gwamnatin Iran da ta zo a rungumi juna, a sasanta kuma a zauna lafiya, kama yadda kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Trump yana cewa: “Dukkanin Sojojin sun tsira daga wannan harin, face barna kalilan da makaman suka yi ma sansaninmu. A shirye sojojin Amurka suke su fuskanci komai. Amma alamu sun nuna Iran ta sauko, wanda hakan abu ne mai kyau ga dukkanin bangarorin dake da ruwa da tsaki, da ma duniya gaba daya. Babu dan Amurka ko dan Iraqi daya mutu.”
Sai dai Trump ya yi nuni da cewa zai kara kakaba ma gwamnatin kasar Iran takunkumi, amma bai yi maganan daukan fansan harin da Iran ta kai sansanin Sojin kasar Amurka ba, ko wani ramuwar gayya ba.
Wannan hari da Iran ta kai ya kasance mataki na farko da ta dauka tun bayan kisan Janar Sulaiman da Amurka ta yi. Sai dai daga karshe Trump ya yi kira ga sauran kasashen duniya da kada su amince da yarjejeniyar nukiliya da aka shiga da Iran.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng