Yanzu-yanzu: Babu Sojan Amurkan da harin Iran ya kashe - Trump

Yanzu-yanzu: Babu Sojan Amurkan da harin Iran ya kashe - Trump

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce babu dan Amurkan da ya samu rauni a harin bama-bamai masu linzamin da Iran ta kai sansanin Sojin Amurka dake Iraqi ranar Laraba.

Trump ya sanar da hakan ne a jawabin da yayi ga kasar a fadar White House.

Yace: "Mutan Amurka su godewa Allah kuma suyi farin cikin cewa babu dan Amurkan da harin daren jiya da Iran ta kai ya shafa."

"Babu wanda ya jikkata, dukkan Sojojinmu na nan cikin koshin lafiya, kuma abubuwa kadan aka lalata a sansanin Sojinmu."

Trump ya yi kira ga kasashen Turai, Rasha, Sin, Jamus da Ingila su fita daga yarjejeniyar nukiliyan da suka shiga a shekarar 2015.

Za ku tuna cewa Kasar Iran ta yi barazanar ragargazan Izra'ila da Dubai idan har kasar Amurka ta sake kai mata kara bayan ta mayar da martani da daren jiya inda ta kaiwa Sojin Amurka hari.

Iran ta harba rokoki masu linzami 20 sansanin Sojin Amurka dake Iraqi domin mayar da martani kan kisan babban kwamandan Iran, Qassem Soleimani, da Amurka tayi ranar Juma'a.

Sansanin Ayn Al Asad da Sansanin Erbil Asad ne aka harba manyan rokokin misalin karfe 5:30 na yammacin Talata kuma da alamun akalla sojojin Amurka 80 sun hallaka.

Hukumar tsaron Iran ta gargadi Amurka kan kokarin ramawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel