Yanzu-yanzu: Kamfanonin jirage duniya sun hana jiragensu bin ta Iran da Iraqi

Yanzu-yanzu: Kamfanonin jirage duniya sun hana jiragensu bin ta Iran da Iraqi

Manyan kamfanonin jiragen duniya a ranar Laraba sun bayyana cewa sun gudun sararin samaniyar Iraqi da Iran domin gudun kada a samu matsala musamman yanzu da Iran ta fara harba rokoki.

Byaan harin da Iran ta kai, hukumar jiragen saman kasar Amurka ta umurci jiragenta su dakatad da duk wani tafiya zuwa kasashen larabawa.

Ta Sararin samaniyar kasashen larabawa jiragen Amurka ke bi domin zuwa kasashen Asiya da Turai. A yanzu, sai dai suyi zagaye.

Yanzu-yanzu: Kamfanonin jirage duniya sun hana jiragensu bin ta Iran da Iraqi
Yanzu-yanzu: Kamfanonin jirage duniya sun hana jiragensu bin ta Iran da Iraqi
Asali: Facebook

Kakakin Air France ya bayyana cewa: "Domin tabbatar da tsaro bisa ga hare-haren da ake kaiwa, Air France ta yanke shawarar dakatad da jiragenta da zasu bi sararin samaniyar Iran da Iraqi."

Hakazalika kakakin kamfain jirgin KLM ya bayyanawa AFP cewa: "Har ila mashaa'a llahu, babu jirgin KLM da zai bi sararin samaniyar Iran da Iraqi."

A Jamus kuwa, kamfanin jirgin Lufthansa ta ce ta dakatad da jirgin Iran da dukkan jiragen da zasu bi ta Iran da Iraqi har sai lokaciin da abubuwa suka lafa.

Ba'a bar Kamfanonin jiragen kasar Dubai, Emirates, da Fly Dubai a baya ba, sun dakatad da dukkan jiragen zuwa Baghdad.

Hakazalika jirgin kasar Australiya, Qantasa, jirgin Singapore, Malaysiya, Vietnam, Jaoan da Hong Kong.

Zaku tuna cewa Iran ta harba rokoki 20 sansanin Sojin Amurka dake Iraqi da yammacin jiya domin mayar da martani kan kisan babban kwamandan Iran, Qassem Soleimani, da Amurka tayi ranar Juma'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng