Allah mai iko: Likitoci sun samu nasarar raba wasu yara da aka haifesu a hade, bayan shafe awa 13 suna tiyata

Allah mai iko: Likitoci sun samu nasarar raba wasu yara da aka haifesu a hade, bayan shafe awa 13 suna tiyata

- Wasu tagwaye da aka haifa a manne da juna sun fara rayuwa a rabe

- Gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyin raba su, inda kwararru suka yi musu aiki a asibitin kasa dake Abuja

- Ministan lafiya, Dr Osagie ya jinjinawa kungiyar kwararrun likitocin da suka yi aikin

Wasu tagwaye da aka haifa a manne da juna sun fara rayuwa a rabe bayan wata kungiyar kwararrun likitoci suka dau sa'o'i 13 suna aikin raba su a Abuja, babban birnin kasar nan.

Goodness da Mercy sun zo a ba-zata da aka haifesu a ranar 13 ga watan Augusta a babban asibitin tarayya dake Keffi a jihar Nasarawa. An haifesu ne ta hanyar yiwa mahaifiyarsu aiki duk da kuwa bata san tana dauke da tagwaye bane. Bayan fito dasu ne aka ga kirjinsu da cikinsu a hade.

An bukaci kusan naira miliyan 20 don yi musu aikin da zasu rabe tun bayan hadewarsu a cikin mahaifa.

Abun farin cikin ya fara ne a lokacin da babban asibitin kasa dake Abuja suka yanke hukuncin yi musu aikin a kyauta. Hakan ne kuwa yayi sanadin aikin da ya raba manannun tagwayen.

A ranar Talata da ministan ilimi ya gabatar da jawabi na musamman a kan rabe tagwayen, Dr Osagie Ehanire ya danganta nasarar wannan aikin da goyon bayan hadaka daga kwararrun da kuma gwamnatin tarayyar da ta dauki nauyi.

KU KARANTA: San barka: Jaruma Rahama Sadau ta kafa gidauniya don samawa almajirai kayan sanyi

Ya ce: "Wadannan kyawawan jariran 'yan asalin jihar Benuwe ne kuma muna matukar alfahari da iyayensu.

"Kungiyar kwararrun da aka ba wannan aikin sun nuna kwarewarsu a fannin lafiya duk da matsakaitan kayan aikin da ake dasu. A hakan kuwa muna da tabbacin cewa zamu kai kololuwa a fannin kiwon lafiya a duniya."

Tun bayan da suka sauka a Abuja, anyi wa tagwayen aiki har sau hudu a bangarori daban-daban na lafiya. Sunyi kuma watanni 16 suna karbar kulawar kwararrun masana a kiwon lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel