Matasa sun yi zanga-zanga kan sakin wasu masu garkuwa da mutane a Adamawa

Matasa sun yi zanga-zanga kan sakin wasu masu garkuwa da mutane a Adamawa

Matasa daga garin Girei na jihar Adamawa sun rufe babban titin Yola-Mubi domin yin zanga-zangan sakin wasu masu garkuwa da mutane da 'yan sanda suka kama.

Daruruwan masu zanga-zangar sun janyo cinkoso a titi na sa'o'i wadda hakan ya janyo wa matafiya wahalwalu sun nemi kwamishinan 'yan sandan jihar ya zo da kansa ya yi musu bayani.

Mai magana da yawun matasan, wanda ke da saruatan Sarkin matasa a Girei, Saidu Hamman Girei ya ce sun samu bayanai masu inganci da ke nuna cewa an saki wasu daga cikin wadanda ake tuhuma da garkuwa da mutane da suka taimakawa 'yan sanda kama su.

Ya koka kan yadda masu garkuwa da mutanen suka kashe mutane 10 sannan sun karbi fiye da Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa a hannun mutane a baya-bayan nan.

Ya yi zargin cewa: "Mun taimakawa jam'an tsaro wurin kama a kalla mutum 11 da ake zargi tare da hujjoji masu karfi amma abinda muke ji shine wai an bayar da umurnin sakinsu daga headkwata."

KU KARANTA: Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

"Muna son kwamishinan 'yan sanda ya zo ya fada mana dalili domin hankalin mutane ya tashi. Ni ne bawa matasa hakuri na hana su kone ofishin 'yan sanda a jiya," inji Hamman-Girei.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya musanta zargin da matasan ke yi inda ya ce a halin yanzu wadanda ake zargi da garkuwa da mutanen suna fuskantar shari'a a kotu.

Nguroje ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar ya umurci mataimakin kwamishina mai kula da ayyuka ya ziyarci garin Girei ya tattauna da matasan don warware matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164