Kaduna: 'Yan bindiga sun tafka ta'asa a harin da suka kai kauyen Bana

Kaduna: 'Yan bindiga sun tafka ta'asa a harin da suka kai kauyen Bana

Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun kai hari kauyen Bana da ke kusa da Buruku a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna inda suka kashe mutane biyu.

Mazauna kauyan da ke cikin firgici suna zullumin cewa maharan sun yi awon gaba da wasu mutane daga kauyen.

Daily Trust ta gano cewa lamarin ya afku ne a ranar Litinin da safe amma saboda rashin kyawun sabis na wayar tarho mutanen kauyen ba su samu damar sanar da hukumomin tsaro ba.

Wani dan banga da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa a lokacin da suka isa kauyen, galibin mutanen kauyen sun tsere daga gidajensu.

Ya ce: "'Yan bindigan sun isa garin ne a kan babura suka kai hari a Bana da ke kusa da garin Buruku. Sun kashe mutane biyu kuma ana fargabar sun sace wasu mutane masu yawa."

DUBA WANNAN: Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

Ya kara da cewa mafi yawancin mutanen kauyen da suka tsere sun koma garin Buruku a halin yanzu.

Dukkan yunkurin da aka yi na ji ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya ci tura domin bai daga wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar-ta-kwana da aka aika masa ba na neman karin bayani a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel