Kotu ta haramtawa gwamnatin tarayya kara farashin wutan lantarki

Kotu ta haramtawa gwamnatin tarayya kara farashin wutan lantarki

Wata babbar kotun tarayya dake Legas ta umurci masu ruwa da tsaki a bangaren wutan lantarki su cigaba da amfani da farashin da aka kai har sai ta yanke hukunci kan lamarin yunkurin kara kudi.

Alkalin ya yanke hakan ne bisa ga karar da wata kungiyar kare hakkin dan Adam suka shigar kan kamfanonin wutan lantarki 15.

Wadanda aka shigar kara sune kamfanonin raba wutan Abuja AEDC, Benin BEDC, Enugu EEDC, Eko EKDC, Ibadan IEDC, Ikeja , Jos , Kaduna KEDC , Kano KEDCO , Port Harcourt da Yola YEDC.

Sauran sune kamfanin lura da wutan lantarki NERC, Kamfanin sayar da wutan lantarki NBET, BPE da ministan wutan lantarki, Saleh Mamman.

Alkali Muslim Hassan ya dage karar zuwa ranar 20 ga watan Junairu, 2020.

Zaku tuna cewa Yan Najeriya sun yi ca kan gwamnatin tarayya yayinda hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC a ranar Asabar ta sanar da karin farashin wutan lantarkin fadin tarayya fari daga ranar 1 ga watan Junairu, 2020.

Shugaban hukumar, Joseph Mohmoh da kwamishanan bada lasisi, Dafe Akpenye, ne suka rattaba hannu kan umurnin.

Amma daga baya, NERC ta yi amai ta lashe inda ta yi bayanin cewa ba ta kara farashin wutan lantarki ba tukun.

Jami'an hulda da jama'a na hukumar NERC, Usman Arabi, ya yi fashin baki kan lamarin a jawabin da ya daura a shafin yanar gizon hukumar ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel