Yanzu-yanzu: Buhari ya soke dakatarwar da aka yi wa shugaban REA

Yanzu-yanzu: Buhari ya soke dakatarwar da aka yi wa shugaban REA

Shugaba Muhammadu Buhari ta soke dakatarwar da aka yi wa Damilola Ogunbiyi a matsayin babban manajan Hukumar samar da lantarki na karkara (REA).

Idan ba a manta ba dai ministan makamashi, Sale Mamman ne ya dakatar da Ogunbiyi.

Ya kuma bayar da umurnin gudanar da bincike a kan zargin aikata ba dai-dai ba a lokacin da ta ke shugabancin hukumar.

Kafin dakatar da ita, Ogunbiyi wacce ita ce shugaba mace na farko a hukumar ta REA, ta mika takardan yin murabus dinta domin ta samu sabon aiki a Majalisar Dinkin Duniya a matsayin wakiliya a fanin samar da makamashi da kuma shugabancin Sustainable Energy for All.

DUBA WANNAN: Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

Duk da shugaban kasar ya soke dakarwar da aka yi mata, ya karbi dakartan ajiye aikinta.

Wasikar ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya aike wa Amina Mohammed, mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya ne ya bayyana umurnin na shugaban kasa ga hukumar ta kasa da kasa.

Wasikar ta ce: "Sakamakon binciken da aka gudanar a fanin makamashi na Najeriya, na rubuto in sanar da ke cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nazarin lamarin kuma ya bayar da umurnin soke dakatarwar da aka yi wa Mrs Damilola Ogunbiyi, shugaban REA saboda rashin bin ka'ida."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel