An sace N16m na albashin mutane a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina

An sace N16m na albashin mutane a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina

Wasu mutane sun yi awon gaba da makudan kudin albashin matasan S-Power a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, The Guardian ta ruwaito.

Rahoton ya bayyana cewa mutanen sun fasa cikin ofishin dake sakatariyar ne a daren Lahadi, 5 ga watan Junairu, 2020.

Yayinda majiyoyi suka ce miliyoyi aka sace, wani majiya mai karfi ya bayyana cewa kudin zai kai milyan goma sha shida (N16m).

Ya kara da cewa an garkame mutane uku da ake zargin suna da hannun cikin fashin ranar Litinin.

KU KARANTA: Jerin Coci-coci 10 da aka mayar Masallatai a duniya

Wadanda aka garkame sune ma'aikatan ofishin sakataren guda biyu, da kuma mai gadin ofishin.

Wannan abu ya faru ne lokacin da aka baiwa ofishin sakataren gwamnatin jihar aikin biyan matasan S-Power dake koyarwa a makarantun Sakandare da Firamare a jihar Katsina.

S-Power wata shirin gwamnatin jihar Katsina data hada hannu da shirin N-Power na gwamnatin tarayya domin daukan matasa da suka kammala karatu aiki a makarantun gwamnati.

An bayyana cewa an ajiye makudan kudi a ofishin sakataren domin biyan matasan kudin alawun.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Gambo Isah da mai magana da yawun sakataren basu mayar da martani kan tambayoyin da akayi musu kan lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel