Za mu debi sabbin ma’aiakata da suka cancanta a NAFDAC – Shugabar NAFDAC

Za mu debi sabbin ma’aiakata da suka cancanta a NAFDAC – Shugabar NAFDAC

Hukumar kula da tsafta da ingancin abinci, NAFDAC, ta bayyana shirinta na diban sabbin ma’aiakata da suka cancanta a shekarar 2020 domin cige gibin ma’aikatan da hukumar ta ke dasu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta sanar da haka yayin da take ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, inda tace akwai karancin ma’aikata a hukumar da zasu aiwatar da ayyukan ta.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Babatun da kake yi zai iya mayar da hannun agogo baya – Hukumar Soji ga Gwamna Zulum

“Muna bukatar karin ma’aikata, muna kuma bukatar ababen hawa, bada jimawa ba muka samu amincewar gwamnati na sayen motoci 15, amma ko kadan ba zasu isa wajen ayyukanmu a jahohi 36 ba. Saboda ba zamu iya baiwa jaha mota daya ba.

“Me mota daya za ta yi a jaha daya wajen bin sawun miyagun mutane dake da manufar kashe yan Najeriya da gurbatattun magunguna, don haka muna ta addua, muna kuma fata tare da tanadan tsare tsaren sayen sabbin motoci a 2020.

“Baya ga motocin ma’aikata, muna bukatar kayan aiki, saboda dasu ake amfani wajen gwaje gwajen magunguna. Daga cikin irin wadannan kayan aiki akwai wanda ya kai naira miliyan 200.” Inji Adeyeye.

A wani labarin kuma, babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu ya tura sabon kwamishinan Yansanda zuwa jahar Kaduna, Umar Muri, wanda ya amshi ragamar iko a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Yakubu Sabo ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, a garin Kaduna, inda yace Muri ya mashi ragamar iko ne daga hannun tsohon kwamishina Ali Janga.

Kaakakin yace an turo Muri jahar Kaduna ne sakamakon Ali Janga zai wuce cibiyar horas manyan jami’an gwamnati dake Kuru, Jos, jahar Filato. Kaakaki Sabo ya kara da cewa Muri ne kwamishinan Yansanda na 38 a Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel