Jana’izar babban kwamandan Sojan Iran: Mutane 35 sun mutu, 48 sun jikkata

Jana’izar babban kwamandan Sojan Iran: Mutane 35 sun mutu, 48 sun jikkata

An samu turmutsitsin jama’a a yayin jana’izar babban kwamandan rundunar Sojan kasar Iran, Janar Qassem Soleimani daya gudana a birnin Kerman na kasar Iran a ranar Talata, 7 ga watan Janairu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito akalla mutane 35 ne suka mutu, yayin da wasu 48 suka samu munana rauni a sakamakon wannan turmutsitsi daya wakana a daidai lokacin da aka gudanar da jana’izar babban kwamanda Soleimani.

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ya tura sabon kwamishinan Yansanda jahar Kaduna

Jana’izar babban kwamandan Sojan Iran: Mutane 35 sun mutu, 48 sun jikkata
Yan Shia a jana'izar Janar Qassem
Asali: UGC

Rahotanni sun tabbatar da cewa dubun dubatan jama’a ne suka yi fitan farin dango domin halartar jana’izar kwamandan, wanda gwamnatin kasar Amurka ta kashe shi a ranar Juma’a ta hanyar kai masa harin Roka yayin da yake cikin motarsa a birnin Bagdad na kasar Iraq.

Sai da aka fara daukan gawar Soleimani zuwa wani birnin kasar Iraqi, daga nan aka zarce da shi zuwa Kerman. Kisan Soleimani ya janyo tashe tashen hankula da zanga zanga a yankin gabas ta tsakiya, tare da jimami a Iran.

Bayan kisan Soleimani, gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa: “Za mu dauki fansa, fansa mai zafi da karfi.” Inji babban kwamandan dakarun juyin juya hali na kasar Iran, Janar Hossein Salami a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban dubun dubatan masu jimami.

Shi ma jagoran kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana cewa zasu dauki fansa, amma sai a lokacin da suka ga dama, kuma a inda suke ganin ya dace. Daga cikin wadanda suka halarci jana’izar akwai Hezbollah da kungiyar Hamas.

Sai dai duk raddin da gwamnatin kasar Iran ta yi, masana na ganin kasar Iran ba za ta taba tarda ta yi fito na fito da gwamnatin kasar Amurka ba, amma a nasa jawabin, shugaban Amurka yace sun zabi wurare 52 da zasu tasa idan har Iran ta kai mata hari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel