Abun al’ajabi: Wani katoton karfe ya rufto daga sararin samaniya a Nijar
Rahotanni sun kawo cewa wani katoton karfe ya fado daga can saurarin samaniya, inda ya sauka a wani kauye da ke garin Tania a yankin Damagaram na kasar Nijar.
An tattaro cewa faruwar wannan lamari ya girgiza mazauna yankin.
A cewar mazauna yankin, sun ji kara mai tsoratarwa tare da ganin gilmawar hasken walkiya jim kadan bayan fadowar karfe a kauyen Tazai.
An rahoto cewa lamarin ya afku ne a ranar 31 ga watan Disamba ta 2019.
Tuni dai gwamnatin Nijar ta tura wata tawaga ta kwararru d hukumomi da jami’an tsaro zuwa yankin don ganin abunda ya faru.
KU KARANTA KUMA: Tanko Yakasai ya caccaki Buhari da APC, ya ce babu abunda ya chanja a Najeriya tun 2015
Daraktan hukumar ma’adinai ta kasar a Damagaram, Na Allah Ousmane, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, a halin da ake ciki wasu kwararru na musamman na gudanar da bincike kan karfen wanda a cewarsa yana da nauyi sosai.
A wani labari na daban, mun ji cewa akalla mutane 30 ne suka mutu a jihar Borno bayan tashin wani bam da aka dana a kan wata gada, majiyoyi suka fada ma Reuters a ranar Litinin.
Bam din ya tashi ne da misalin karfe 5:00 na yamma a gadar da ke cike da mutane a kasuwar garin Gamboru da ya shiga har kasar Kamaru.
Idanun shaida a kasuwar sun ce an kai sama da mutane 35 da suka jikkata zuwa asibiti biyo bayan harin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng