Wutar lantarki ta illata barawon taransifoma

Wutar lantarki ta illata barawon taransifoma

- Wani mutum mai suna Wasiu Ibrahim ya samu munanan raunika bayan da yayi yunkurin lalatawa da satar taransfoma

- Wanda ake zargin ya fado kasa warwas tare da miyagun kuna a jikinsa bayan da yayi kokarin satar sata tare da lalata wasu sassan taranfomar

- Tuni 'yan sandan yankin suka cafke wanda ake zargin tare da mika shi ofishinsu don amsa tambayoyi

Wani mutum mai suna Wasiu Ibrahim ya samu munanan raunika bayan da yayi kokarin lalatawa tare da satar taransfoma a yankin Araromi dake babban titin Ilesa zuwa Akure a jihar Osun.

Wanda ake zargin ya fado kasa warwas tare da miyagun kuna a jikinsa bayan da yayi kokarin satar taransfomar ta hanyar lalata wasu sassa nata.

Mazauna yankin sun bayyana cewa sun ga mutumin yayin da yazo satar taransfomar da lalata wasu sassa nata, amma sai tartsatsin wuta ya watsar dashi gefe kuma ya samu raunika.

DUBA WANNNAN: Kissan Soleimani: NSCIA ta gargadi matasan Najeriya kan yin zanga-zanga

An kai lamarin gaban babbar hedkwatar ‘yan sanda dake Ijebu-Jesa kuma ‘yan sandan sun hanzarta isa wajen da lamarin ya faru tare da kai shi babban ofishin nasu don amsa tambayoyi.

Babbar jami’ar rarraba wutar lantarki ta jihar Oyo, Kikelomo Owoaye ta tabbatar da aukuwar lamarin

Owoeye ta ce, “Muna mika godiyarmu ga jama’ar yankin Araromi wadanda suka taimaka wajen tsare barawon taranfomar wanda ya raunata sakamakon tartsatsin wutar lantarkin da ke baiwa yankin wuta”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel