Babban sufetan Yansanda ya tura sabon kwamishinan Yansanda jahar Kaduna

Babban sufetan Yansanda ya tura sabon kwamishinan Yansanda jahar Kaduna

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu ya tura sabon kwamishinan Yansanda zuwa jahar Kaduna, Umar Muri, wanda ya amshi ragamar iko a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Yakubu Sabo ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, a garin Kaduna, inda yace Muri ya mashi ragamar iko ne daga hannun tsohon kwamishina Ali Janga.

KU KARANTA: Ragas: Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’addan Boko Haram 6, an kashe musu 4

Babban sufetan Yansanda ya tura sabon kwamishinan Yansanda jahar Kaduna
Umar Muri
Asali: Facebook

Kaakakin yace an turo Muri jahar Kaduna ne sakamakon Ali Janga zai wuce cibiyar horas manyan jami’an gwamnati dake Kuru, Jos, jahar Filato. Kaakaki Sabo ya kara da cewa Muri ne kwamishinan Yansanda na 38 a Kaduna.

Umar Muri ya fito ne daga garin Muri, cikin karamar hukumar Karim Lamido na jahar Taraba, ya yi karatun sharia a jami’ar Maiduguri ta jahar Borno, sa’annan ya samu horo a fannin shari’a a makarantar lauyoyi dake Legas.

Muri ya fara aiki da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya a matsayin mashwarci a kan harkar shari’a, daga bisani kuma ya shiga aikin Dansanda a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1990.

Muri ya rike mukamai daban daban da suka hada da Kaakakin rundunar Yansandan jahar Anambra 1992-1997, hadimin mataimakin sufetan Yansanda Bukar Ali 1999-2002, hukumar EFCC 2008-2009 da sauran ayyuka daban daban.

Kafin wannan sabon mukamin daya samu, Muri ne kwamishinan Yansanda dake kula da saye saye a shelkwatar rundunar Yansandan Najeriya.

A wani labari kuma, dakarun runduna ta 29 ta rundunar sojan kasa ta Najeriya ta hallaka mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram guda shida a wani arangama da suka kwasa da juna a kauyen Jakana na karamar hukumar Konduga na jahar Borno.

Sojoji da Boko Haram sun yi wannan arangama ne a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu inda aka kusan yin ragas, sakamakon Sojoji sun kashe yan ta’adda shida, Boko Haram kuma ta kashe Sojoji 4.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng