Wasu shafaffu da mai ne ke hana yan Najeriya samun wutar lantarki – Minista
Ministan lantarki, Mamman Saleh dan mutan Taraba ya bayyana cewa akwai wasu shafaffu da mai da suka dage suka tubure tare da dogewa a kan hana yan Najeriya samun isashshen wutar lantarki.
Jaridar The Cables ta ruwaito ministan ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani game da batun sallamar wasu manyan jami’an ma’aikatar wutar lantarkin da suka hada da Damilola Ogunbiyi da Marilyn Amobi.
KU KARANTA: Yan bindiga sun bude wuta a Malumfashi, sun bindige Malamin SBRS har lahira
Damilo Ogunbiyi ne tsohon daraktan hukumar samar da wutar lantarki a karkara, yayin da Marilyn Amobi ta kasance dakatacciyar shugaban hukumar wutar lantarki na Nigerian Bulk Electricity Trading Plc, NBET, sai dai an zargi ministan da nuna bambamcin kabilanci wajen dakatarwar.
Amma a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu ministan ya musanta wannan zargi, inda yace ya dauki wannan mataki ne don kare hakkin yan Najeriya, saboda a cewarsa akwai wasu shafaffu da mai a ma’aikatar lantarki da suke dakile duk wani yunkuri da gwamnati ke yi na samar da wutar lantarki a Najeriya.
Ministan da ya yi magana ta bakin hadiminsa, Aaron Artimas, yace: “Kamata ya yi yan Najeriya su damu da dalilin da yasa aka gaza samun wuta a Najeriya duk da biliyoyin dalolin da aka kashe domin samar da wutar?
“Wannan lamari ya yi matukar shafar aikin ma’aikatar wajen samar da wutar lantarki, babu wani shugaba da zai lamunci irin wannan zagon kasar, balle har ya samu nasara. Tun bayan da ya zama minista watanni 5 da suka gabata, Mamman ya san aikin ba zai zama mai sauki ba.
“Jim kadan da hawansa muka fara samun labarin wasu shafaffu da mai a ma’aikatar dake hana yan Najeriya samun wutar lantarki, tun a watan Nuwamba wadannan shafaffu da mai suka fara amfani da wasu kungiyoyi suna rubutun batanci ga ministan.” Inji shi.
Daga karshe Ministan yace mutanen su ne kuma wadanda basu kaunar ganin an kawo wani canji a ayyukan ma’aikatar domin inganta ayyukanta, don haka yace ba zasu lamunci irin wadannan mutane da basu da wata manufa illa cigaba da rike mukamai ba yi ma jama’a aiki ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng