Gwamnan Filato ya musanta amincewa da biyan sabon karancin albashin N30,000

Gwamnan Filato ya musanta amincewa da biyan sabon karancin albashin N30,000

Gwamnatin jahar Filato ta musanta batun da ake yayatawa na cewa wai ta amince za ta biya sabon karancin albashin N30,000 kamar yadda saura takwarorinta musamman na yankin Arewacin Najeriya suka yi.

Gwamnatin ta bayyana haka ne saboda a cewarta har yanzu kwamitin da ta kafa tun a watan Nuwambar 2019 da zai tattauna da kungiyar kwadago domin tsara yadda za’a aiwatar da sabon albashin bai kammala zaman tattaunawar ba.

KU KARANTA: Masu garkuwa sun yi awon gaba da matafiya guda 10, sun kashe 1 a Taraba

Gwamnatin ta bayyana haka ne ya bakin kwamishinan watsa labaru na jahar, Dan Manjag, inda yace labarin dake yawo a kafafen sadarwar zamani na cewa wai gwamnatin ta amince da biyan sabon karancin albashin 30,000 ba gaskiya bane.

“Babu bukatar tattaunawa da wani kungiya ko mutum kafin gwamnati ta fara aiwatar da dokar, amma gwamnati ta kafa kwamitin tattaunawa da kungiyar kwadago ne domin duba yiwuwar dabbaka dokar a jahar duba da yanayin lalitar kowacce jaha kamar yadda gwamnatin tarayya ta umarta.” Inji shi.

Daga karshe ya tabbatar da manufar gwamnatin na kula a walwalar ma’aikatan jahar Filato, sa’annan ya yi kira ga ma’aikata da kungiyoyinsu dasu kwantar da hankulansu yayin da ake cigaba da tattaunawa.

A wani labarin kuma, hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari, JAMB ta tsayar da ranar 13 ga watan Janairu a matsayin ranar da za ta fara sayar da takardar sha’awar zana jarabawar na shekarar 2020 ga dalibai masu sha’awa.

Shugaban sashin watsa labaru na hukumar, Fabian Benjamin ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, 5 ga watan Janairu yayin da yake ganawa da manema labaru a jahar Legas, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito.

A cewar Benjamin, hukumar ta kammala shirye shirye da duk wasu tsare tsaren fara sayar da takardar JAMB na bana daga ranar Litinin, 13 ga watan Janairu zuwa ranar Litinin, 17 ga watan Feburairu, a duk fadin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng