Yan Boko Haram sun kai hari Chibok, sun hallaka mutane 3

Yan Boko Haram sun kai hari Chibok, sun hallaka mutane 3

Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka mutane uku kuma sun yi awon gaba da babura a wani kauyen karamar hukumar Chibok dake jihar Borno. Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna garin sun bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun dira garin Bila-Amboldar ne misalin karfe 10 na dare a ranar Juma'a kuma suka fara bankawa gidajen mutane wuta.

Daga baya suka fara bindige masu kokarin guduwa inda suka kashe yan uwa biyu, James Kwakwi da Mutah Kwakwi da wani mutum, Yusuf Yakubu, wanda ya dawo daga Legas kwanan nan domin ganin iyalansa.

Wata mazauniyar garin mai suna, Mana Bila, tace yan ta'addan sun ajiye baburansu a kauyen Makalama dake makwabtaka dasu, bayan mutan garin sun gudu daga muhallansu sakamakon hare-hare.

Ta kara da cewa yan ta'addan sun yi awon gaba da babura sama da 20 da kuma wasu kayan alfanu.

Shugaban kungiyar iyayen yan matan Chibok, Yakubu Nkenki, ya bayyanawa Dailty Trust cewa har yanzu mutan garin na jimamin rashin mazajensu yayinda ya kai gaisuwar ta'aziyya.

Yace: "Abin da ban takaici, an jefa kauyen cikin jimami bayan sun yi rashin majiya karfi uku. Sun fada min cewa yan bindigan sun yi awon gaba da babura 24 da mata biyu amma daga baya sun sakesu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel