Gwamnan Bauchi ya gano sunayen matattu 596 masu karban albashin aikin gwamnati

Gwamnan Bauchi ya gano sunayen matattu 596 masu karban albashin aikin gwamnati

Kwamitin lamban asusun bankin bai daya BVN ta bankado sunayen matattun ma'aikata 596 dake karban albashin aikin gwamnatin har yanzu.

Za ku tuna cewa gwamnan jihar, Bala Mohammed, ya kafa kwamitin bankado ma'aikatan bogi da yan fanshon karya dake amsan albashin aikin gwamnati cikin watanni uku.

Shugaban kwamitin, Adamu Gumba, yayinda yake hira da manema labarai ranar Litinin a Bauchi ya bayyana cewa an gayyaci ma'aikatan gwamnatin jiha da na kananan hukumomi da yan fansho 30, 226 domin tantancesu.

Amma daga baya, mutane 24,736 kadai suka gabatar da kansu, an nemi 4,578 an rasa.

Yace: "Daga cikin mutane 30,226 da aka tantance, mutane 24,736 kadai suka tsira. Mun gano 596 sun mutu."

"Ga wadanda basu gabatar da kansu ba, da yiwuwan za'a sake basu wani dama. Ina ganin suna da kashi a gindi kuma wajibi ne a ganosu."

"Idan aka tantance dukkan ma'aikata da yan fanshon jihar 130,000, za'a bankado na bogi da dama tunda har muka samu wannan yawan cikin 30,226 kadai."

Ya tabbatar da cewa dukkan wadanda aka tantance da basu samu albashinsu da alawus na watanni uku ba za su ji kararrawa ba tare da dadewa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel