Yan bindiga sun yi awon gaba da yan kasuwa akalla 30 a Batsari

Yan bindiga sun yi awon gaba da yan kasuwa akalla 30 a Batsari

Wasu yan bindiga sun kai farmaki kauyen Ruma, a karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina ranar Lahadi, 5 ga watan Junairu, 2020, kuma sukayi awon gaba da mutane da dama. Channels TV ta ruwaito.

Mazauna kauyen sun bayyanawa manema labarai a wayan tarho cewa yawancin wadanda aka sace da yammacin Lahadi yan kasuwa ne dake hanyarsu ta dawowa bayan cin kasuwar Jibiya.

Sun bayyana cewa akalla mutane 30 aka waske.

Amma kakakin hukumar yan sandan jihar, Gambo Isah, ya jaddada cewa adadin wadanda aka sace bai kai haka ba, an karawa aya siga.

A cewarsa, yan bindigan kimanin 60 dauke da bindigogi AK47 suka tare manyan motoci biyu a hanyar Jibiya zuwa Batsari kuma sukayi awon gaba da fasinjojin zuwa cikin daji.

Ya kara da cewa jami'an atisayen Puff Adder sun bazama neman yan ta'addan kuma sun ceto dukkan mutanen illa mutane bakwai.

Isah ya tabbatar da cewa yan sanda sun yi dajin zobe domin sauran bakwan da suka rage.

A wani labarin daban, Hukumar yan sandan jihar Kano ta damke wata matar aure, Hauwa Lawal, kan laifin jefa kishiyarta, Zuwaira Sani, da dan goyonta, Mustafa Gambo, cikin rijiya a jihar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da damketa a hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Lahadi.

Haruna ya bayyana cewa hukumar ta samu rahoto ranar Juma'a cewa wata mata mai suna Hausa a kauyen Rurum dake karamar hukumar Rano ta tunkuda dan kishiyarta cikin rijiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel