An damke matar da ta tunkuda kishiyarta da dan goyonta cikin rijiya a Kano

An damke matar da ta tunkuda kishiyarta da dan goyonta cikin rijiya a Kano

Hukumar yan sandan jihar Kano ta damke wata matar aure, Hauwa Lawal, kan laifin jefa kishiyarta, Zuwaira Sani, da dan goyonta, Mustafa Gambo, cikin rijiya a karamar hukumar Rano ta jihar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da damketa a hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Lahadi.

Haruna ya bayyana cewa hukumar ta samu rahoto ranar Juma'a cewa matar mai suna Hauwa a kauyen Rurum dake karamar hukumar Rano ta tunkuda dan kishiyarta cikin rijiya.

Bayan aikata wannan aika-aika, Hauwal Lawal, ta arce daga gidan kuma aka fara nemanta ruwa a jallo.

Haruna yace misalin karfe 1:17 na daren Asabar jami'an atisayen Puff Ader sukayi ram da ita.

DUBA NAN: Yan sanda 103 aka kashe a shekarar 2019 - Lissafi

Yace: "Matar ta samu sabani da kishiyarta. Kawai sai suka fara fada a cikin gidan, sai ta jefa kishiyarta dake goye da danta mai watanni 18 da haihuwa, Mustafa Gambo, cikin rijiyan dake gidan."

"Daga baya aka ciro matar da 'danta daga cikin rijiyan kuma aka garzaya da su asibitin Rano inda aka tabbatar da mutuwar matar amma 'danta goyonta ya rayu kuma an sallamesu daga asibiti."

"Muddin muka kammala bincike, za'a gurfanar da ita a kotu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel