Yan sanda 103 aka kashe a shekarar 2019 - Lissafi

Yan sanda 103 aka kashe a shekarar 2019 - Lissafi

Wani lissafin ajiya da jaridar Daily Trust tayi ya nuna cewa akalla yan sanda 101 suka rasa rayukansu a bakin aiki daga Junairu zuwa Disamba a shekarar 2019.

Legit.ng ta kara da cewa akwai dan sanda daya kashe abokin aikinsa, sannan ya bindige kansa a unguwar Dutse Alhaji dake birnin tarayya Abuja. Hakan ya kara yawansu zuwa 103.

Yan sandan 103 sun mutu ne faggen fama ta hanyar yaki da yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane, yan bindiga dadi, barayin shanu, da kuma yan Boko Haram.

Najeriya na da jami'an yan sanda 400,000. Shugaba Buhari ya baiwa sifeto janar IG Mohammad Adamu umurnin daukan sabbin yan sanda 10,000 a wannan shekaran.

Ga jerin jihohi da yawan yan sandan da aka kashe:

Rivers: 12

Bayelsa: 10

Edo: 10

Kaduna: 8

Taraba: 7

Legas: 5

Akwa Ibom: 5

Abia: 4

Cross River: 4

Kogi: 4

Anambara: 3

Nasarawa: 3

Katsina: 3

Plateau: 3

Sokoto: 3

Zamfara: 3

Ekiti: 2

Kwara: 2

Ondo: 2

Osun: 2

Borno: 1

Delta: 1

Abuja: 3

Kano: 1

Niger: 1

Ogun: 1

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

https://youtu.be/xySbhbh5YLA

Asali: Legit.ng

Online view pixel