Sunaye: Ganduje ya nada sabbin hadimai 17

Sunaye: Ganduje ya nada sabbin hadimai 17

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nada sabbin masu bashi shawara na musamman guda 7 da kuma manyan masu bashi shawara na musamman guda 10.

Ya bukaci sabbin hadiman da ya nada su zage dantse domin yin aiki tukuru da zai taimaki gwamnati ta cimma manufofinta.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da sakataren yada labarai a ofishin gwamna, Abba Anwar, ya aike wa kafafen watsa labarai a Kano ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, sabbin masu bayar da shawarar da aka nada sun hada da; Alhaji Abubakar Sahabo Bawuro (mai bayar da shawara a bangaren kanana da manyan masana'antu, Alhaji Mamudu Sani Madakin Gini (mai bayar da shawara a bangaren harkokin kasuwanci), Isa Yunusa Danguguwa (mai bayar da shawara a bangaren da suka shafi kwadago).

DUBA WANNAN: Hunturu: Yadda garwashin dumama daki ya halaka samari biyu

Salihu Tanko Yakasai (mai bayar da shawara a bangaren kafafen yada labarai), Habibu Sale Mailemo (mai bayar da shawara a bangaren samun kudin shiga), Tasi'u Rabi'u Fanisau (mai bayar da shawara a bangaren harkokin sa suka shafi majalisa) da Alhaji Ahmadu Haruna Zango (mai bayar sa shawara a kan kula da tsaftar kayan abinci).

Jawabin ya kara da cewa, manyan sabbin masu bayar da shawarar da ya nada sun hada da; Ahmed Abbas Ladan (harkokin cikin gida), Auwalu Lawan Shuaibu (fasahar zamani), Ibrahim Abubakar Dantayo Makole (harkokin samar da ruwa), Habib Yahaya Hotoro (SDGs), Omowunmi Shona (harkokin cikin gida II), Tijjani Danlami Maikwano (harkokin matasa) da Jafaru Ahmed Gwarzo (tsaftar muhalli).

Sauran sun hada da Zainab Yayannan Dawakin Tofa (harkokin mata), Zulyadaini Sidi Mustapha (raya karkara) da Musa Kambai (harkokin cikin birni).

A cewar sanarwar, nadin sabbin masu bayar da shawarar ya fara aiki nan take.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel