Zargin Damfara: Babu abinda ya taba hada ni da Shehu Sani - Shugaban Alkalan Najeriya

Zargin Damfara: Babu abinda ya taba hada ni da Shehu Sani - Shugaban Alkalan Najeriya

Shugaban Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad, ya nisanta kasan daga Sanata Shehu Sani wanda ke tsare a yanzu a ofishin hukumar hana almunndahana da yiwa tattalin arzikin kasa EFCC.

A makon da ya gabata, EFCC ta damke Shehu Sani kan zargin karban kudi $20,000 hannun mai kamfanin motoci ASD Motors, Alhaji Sani Dauda, da sunan kaiwa shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

Bugu da kari, an zargi Shehu Sani da taimakawa Alhaji Sani Dauda wajen juya shari'o'i a kotu saboda kusancinsa da shugaban Alkalai CJN Tanko da wasu Alkalai.

Amma a martanin kar ta kwana, CJN Tanko Muhammad ya karyata zargin inda yace bai taba haduwa da Shehu Sani ba a rayuwarsa.

DUBA NAN Mun gano hanyoyi 35 da zamu kaiwa Amurka da Izra'ila hari - Iran

Ya ce da ban mamaki wasu mutane na kokarin bata masa suna don wani manufa ta su.

Ya lashi takobin cewa zai dau mataki kan wadanda ke kokarin bata masa suna saboda hakan ya zama darasi ga ire-irensu.

Kakakin kotun kolin Najeriya, Festus ya bayyana cewa: "Mun samu labarin rahoton da ke yawo a kafofin yada labarai inda ake cewa Shehu Sani ya nemi milyan hudu hannun Alhaji Sani Dauda ASD da sunan zai baiwa Alkalain alkalan Najeriya, Dakta Ibrahim Tanko Muhammad, domin biyan wasu Alkalai kan shari'o'i dake da kura."

"A sani cewa idan har Shehu Sani ne ya fadi hakan, toh karya ne kuma rashin kunya ne da rainin hankali na kokarin batawa shugaban Alkalai suna."

"Muna gudanar da bincike kuma zamu dau mataki bayyan hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel