Mun gano hanyoyi 35 da zamu kaiwa Amurka da Izra'ila hari - Iran

Mun gano hanyoyi 35 da zamu kaiwa Amurka da Izra'ila hari - Iran

Kwamandan Sojin yankin Kerman na kasar Iran, Gholamali Abuhamzeh, ya bayyana cewa kasarsa ta gano akalla wurare 35 da za ta kai harin ramuwar gayya ga Amurka kan kisan Qassem Soleimani.

Reuters ta ruwaito AbuHamzah da cewa nan ba da dadewa ba Iran zata kai mumunan harin jiragen ruwan Amurka.

"Hurmuz wuri ne mai muhimmanci ga Amurka kuma jiragen ruwan Amurka na wucewa ta wajen.. Akwai cibiyoyin Amurka 35 dake yankinmu da Tel Aviv, da zamu iya kai hari."

Sakataren wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce Amurka zata kara hallaka mutane masu muhimmanci a Iran muddin ta kaiwa Sojojin Amurka hari.

Za ku tuna cewa Kasar Amurka ta kai mumunan harin jirgin sama domin hallaka babban kwamandan kasar Iran, Qassem Soleimaini da kwamandan rundunar Kata’ib Hezbollah na Iraqi, Abu Mahdi Muhandis.

Hedkwatar hukumar Sojin Amurka, Pentagon, ta tabbatar da hakan a jawabin da ta saki cewa lallai harin Amurka ya kashe kwamandan rundunar Al-Quds na Iran, Qassem Soleimani, a filin jirgin saman Baghdad dake Iraq.

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, ya bayyana cewa kasar Iran da abokanta za su mayar da martani mai zafi kan ta'addancin Amurka na kisan kwamandanta.

Hakazalika, shugaban koli na Iran, Ayatollah Ali Khameini, ya sanar da cewa za'a kwashe kwanaki uku ana zaman makoki kuma sai an mayar da martani mai tsauri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel