Mutane 8 masu karfin iko a gwamnatin Buhari

Mutane 8 masu karfin iko a gwamnatin Buhari

Ba sabon abu bane idan aka ce akwai wasu mutane masu matukar karfin iko a mulki ko gwamnatin shugaba Buhari. Wadannan mutanen da yawa daga ciki jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC ne, kuma aiyukansu na bayyana cewa ba za a taba tambayarsu a kan wani abu da suka yi ba ko hukunta su.

Wasu daga cikinsu kuwa mutane ne da suka taka rawar gani wajen tabbatar hawan shugaban kasan mulkin Najeriya. Wasu kuwa daga ciki amintattun abokansa ne da suka tabbatar da cikar burin shi.

Ga mutane 8 da suke da matukar karfin iko a mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

1. Aisha Buhari

Itace uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ita ce ta farko a wannan jerin. Itace mutum mafi kusanci da shugaban kasar don kuwa ko wata alfarma ake nema, ana iya bi ta hannunta don samu.

2. Nasir El-Rufai

Shine gwamnan jihar Kaduna kuma yana da karfin iko a mulkin kasar nan. Kusancinsa da shugaban kasa na da yawa don kuwa yafi kowanne gwamna kai ziyara fadar shugaban kasan. Ya taka rawar gani wajen tabbatuwar Buhari a kujerarsa.

3. Ibikunle Amosun

Gwamnan jihar Ogun ne kuma makusancin shugaba Buhari tun kafin ayi majar jam’iyyu. Majiya da dama sun ce, Amosun ne ke zagayawa da Buhari a jihar Legas matukar ya kai ziyara.

DUBA WANNAN: Kishi: Yadda wata mata ta tura kishiyarta cikin rijiya

4. Theophilus Danjuma

Yana daya daga cikin mashahuran masu arziki kuma tsohon soja ne. Yana daga cikin wadanda suka dau nauyin kamfen din shugaban kasa Buhari. Karfin ikonsa a siyasar Najeriya yasa yake daga cikin masu fadi a ji a wannan gwamnatin.

5. Mamman Daura

Daura da ne a wajen Buhari kuma tare suka tashi a matsayin abokai kuma aminan juna. Yana da hannu a duk hukunci ko kuma wani babban nadi da shugaba Buhari yake yi.

6. Isma’ila Funtua

Wannan babban aboki ne ga shugaba Buhari. Duk da bashi da wani mukami a gwamnati, amma yana daga cikin na hannun daman shugaba Buhari.

7. Abba Kyari

Shine shugaban ma’aikata kuma babban mai juya akalar fadar shugaban kasa. Duk wata ziyara da za a yi zuwa shugaban kasa sai ta bi ta hannunsa. Hatta ministoci sai ta hannunsa suke iya isa wajen shugaban kasan.

8. Alhaji Aliko Dangote

Bai kamata hakan ya zama abun mamaki ba saboda babban dan kasuwa ne. Shine mafi arziki a duk fadin nahiyar Afirka. Duk da baya bayyana a matsayin dan siyasa, yana da hannu sosai a yadda akalar gwamnatin kasar nan ke tafiya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel