Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta kara farashin wutan lantarki da kusan ninki daya

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta kara farashin wutan lantarki da kusan ninki daya

Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC a ranar Asabar ta sanar da karin farashin wutan lantarkin fadin tarayya fari daga ranar 1 ga watan Junairu, 2020.

Hukumar ta umurci dukkan kamfanonin raba wutan lantarki 'Discos' tun ranar 31 ga Disamba, 2019 amma sai yau ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

Shugaban hukumar, Joseph Mohmoh da kwamishanan bada lasisi, Dafe Akpenye, ne suka rattaba hannu kan umurnin.

Wadanda wannan kari kari ya shafa sune kamfanin raba wutan Abuja AEDC, Benin BEDC, Enugu EEDC, Eko EKDC, Ibadan IEDC, Ikeja , Jos , Kaduna KEDC , Kano KEDCO , Port Harcourt da Yola YEDC.

Ga yadda sabon farashin yake na jihohi daban-daban:

Ikeja: Daga N13.34 zuwa N21.80 ga kWh daya

Enugu: Daga N17.42 zuwa N30.93 ga kWh daya

Abuja: Daga N27.20 zuwa N47.09.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel