Zargin kisan kai a Kano: Kotu ta ba dan bautar kasa masauki a gidan gyaran hali

Zargin kisan kai a Kano: Kotu ta ba dan bautar kasa masauki a gidan gyaran hali

Wata kotun majistare dake zama a Noman's land a ranar Juma'a, ta bukaci da a adana mata wani dan bautar kasa mai suna Jepthan Peter Makwin dake hidimar kasa a karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano, dake fuskantar zargin kisan yaro mai shekaru 8.

Kotun ta bukaci a adana mata dan bautar kasar ne har zuwa ranar hudu ga watan Fabrairu, lokacin da za a fara sauraron bukatar belinsa.

Idan zamu tuna, wani dan bautar kasa mai suna Jepthan Peter Makwin ya shiga hannun jami'an tsaro saboda zarginsa aka yi da dukan wani yaro mai suna Hassan Sulaiman, mai shekaru takwas a duniya. Bayan shan mugun dukan ne yaron dan aji uku a makarantar firamare ya ce ga garinku a ranar Alhamis, a cikin watan Oktoba a garin Bebeji.

Kamar yadda shugaban NYSC na Kano, Alhaji Ladan Baba ya bayyana, yace lamarin ya faru da rana ne.

DUBA WANNAN: Ma'aikata sun harbe wasu Zakuna uku da suka yi kalaci da gawar wani mutum

"Cikin alhini muke sanar da cewa, lamarin ya faru ne wajen karfe 3:17 na ranar Alhamis, 25 ga watan Oktoba a karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano. Jepthan ya bi yaron ne bayan da yaje katsar mangwaro a wajen dakunan 'yan bautar kasan." ya ce.

Shugaban NYSC na jihar ya kara da cewa, "A hakan ne yaron ya fadi tare da buga kanshi da bangon dake hanyar shiga rukunin dakunan. A take aka nufa asibiti dashi amma daga baya sai yace ga garinku."

A zaman kotun da aka yi a ranar Juma'a, lauyan wanda ake kara ya bukaci belin wanda ake zargin a gaban mai shari'a Fatima Adamu, lamarin da Barista Nasiru Aminu Fagge ya kalubalanta.

Bayan alkalin ta kammala jin ta bakin duk lauyoyin, ta dage sauraron baukatar belin har zuwa ranar 4 ga watan Fabrairu na 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel