Yanzu-yanzu: Fashewar gas ta yi sanadiyar rasa rayuka a Kaduna

Yanzu-yanzu: Fashewar gas ta yi sanadiyar rasa rayuka a Kaduna

Mutane da dama sun rasa rayukan su sakamakon fashewar bututun gas a unguwar sabon tasha da ke Kaduna a safiyar ranar Asabar 4 ga watan Janairu.

Lamarin ya faru ne a wani shago da ke kallon gidan man fetur na Total da ke Sabon Tasha a Kaduna.

Karar fashewar bututun gas din ya razana mutane da gidajensu ke kusa da wurin inda su kayi tsamanin fashewar bam ce ko harin Boko Haram.

Philip Kambai, daya daga cikin wanda ya tsira daga fashewar bam din ya shaidawa The Cable cewa yana cikin wani shagon aski ne da ke kusa da shagon sayar da gas din tare da wasu mutane uku da suka zo yin aski a lokacin da abin ya faru.

DUBA WANNAN: Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

Kambai ya ce, "Ina hanyar fita bayan an gama min aski ne lokacin da na ji kara bum! Na fadi kasa amma na tashi da kyar na haura katanga garin hakan na ji rauni. Wani mutum shima ya haura katangar amma bana tsamanin mai askin da sauran mutane biyun sun fito."

Fashewar gas din ya tarwatsa jikin wadanda suka rasu kamar yadda muka ka jami'an tsaro na tattara sassan jikinsu da ya bazu a titi.

An kuma ce fashewar gas din ta yi sanadiyar rasuwar wani mutum da ya ajiye motarsa a gefen titi don ya yi aski a shagon askin da ke kallon shagon gas din.

Shagon da gas ya ke ya kone kurmus amma jami'an kwana-kwana sun yi kokari sun kashe wutar domin kada ta yadu zuwa sauran sassan ginin.

Kawo yanzu dai 'yan sanda ba su fitar da sanarwa game da afkuwar lamarin ba a lokacin hada wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel