Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

Wani barawo a jihar Legas da ya kware a sane da yankan aljihu ya bayyana yadda yake yanka zakara bayan kowanne kwanaki uku don zoben tsafinsa ya kasance da rai.

Wanda ake zargin mai shekaru 25, ya shiga hannun runduna 'yan sanda ta musamman ta jihar Legas. Yace: “Wani malami ne ya bani zobban hannuna. Ya ce in siyo zakaru biyu da tattasai tare da sauran kayan hadin. A gabana ya kashe zakarun tare da zuba jininsu a kan zobban da sauran kayayyakin da na siyon. Bayan nan ne ya bani su kuma ya bukaci N50,000 na aikinsa.”

Barawon ya cigaba da bayyana cewa, a lokacin da ya karba zobban, bashi da kudin biya. Amma sunyi da malamin cewa zai biya shi kudinshi idan zobban suka fara kawo kudi.

Malamin ya sanar da wanda ake zargin cewa zai yi tafiya zuwa Togo, amma zai karba hakkinshi idan ya dawo. Daga nan kuwa bai kara jin labari ko ganin wannan malamin ba.

DUBA WANNAN: Yadda mutane ke hijira zuwa kan duwatsu bayan harin da Boko Haram ta kai Adamawa

“Amma kafin ya tafi, yace in dinga yi wa wadannan zobban yanka da zakara daya a kowanne kwanaki uku. Ya kara da jan kunne na da kada in kuskura in ci miyar yauki kuma kada in kwanta da mace a yayin da take jinin al’ada.” Ya ce.

Ya kara da cewa, a duk lokacin da ya taba mutum, kudi ko kadara dake jikinsa ko jaka kan koma wajenshi. Akwai lokacin da ya taba kwashe wa wata mata $8,000 ba tare da saninta ba.

Kamar yadda barawon ya sanar, “A ranar da aka kama ni, naga hayaki na fita daga aljihun wani mutum, wannan kuwa alama ce dake nuna cewa akwai kudi a tare dashi. Amma da nayi kokarin taba shi, sai ya fara kalubalanta ta yana cewa ni dan koyo ne a wannan harkar. A take ya tara min jama’a kuma ‘yan sanda suka kama ni.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel