Kuda wajen kwadayi: Budurwa ta goge lambar wani mutumi bayan yayi kuskuren tura mata Naira miliyan 1 cikin asusunta

Kuda wajen kwadayi: Budurwa ta goge lambar wani mutumi bayan yayi kuskuren tura mata Naira miliyan 1 cikin asusunta

- Halin rashin halacci da cin amana a jinin wasu yake, hakazalika butulcin wasu yafi karfin a bada labari

- Wata budurwa ta bukaci saurayi ya tura mata N95,000, amma sai yayi kuskure ya tura N950,000

- Bata kuwa yi wata-wata ba ta toshe lambar wayarshi. Amma da yake akwai alhaki, sai yaci karo da ita a gabar teku tana shakatawa da guminshi

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana halin butulci da cin amana ga saurayinta. Duk da dai saurayin ba na waje bane, dan uwanta ne na jini amma bai sani ba.

Tsohuwar sarauniyar kyau, Cassandra ta bayyana yadda ta damfari dan uwan nata da ya dawo daga kasar ketare a cikin kwanakin nan.

Kamar yadda Cassandra ta sanar, ba a fi sati daya da suka hadu ba, sai ta bukaci ya bata naira dubu dari. Babu bata lokaci ya bata wannan kudin.

Bayan kwanaki kalilan ne ta bukaci ya bata naira dubu casa’in da biyar don zata gyara gashin kanta. A nan ne kuwa aka fara samun babbar matsalar.

Dan uwan nata wanda kuma likita ne, ya turo mata dubu dari tara da hamsin a maimakon dubu casa’in da biyar din. Amma yayi hakan ne bisa ga kuskure.

KU KARANTA: Yadda ake kai 'yan acaba cikin makabarta ana basu wajen kwana a ciki a birnin Abuja

A lokacin da yayi kokarin kiranta don ta mayar mishi da kudinshi, sai ta rufe layin wayarshi daga shiga wayarta.

Amma kuma da yake Allah ba azzalumin bawa bane, sai alhakinshi ya kamata. Taje bakin teku shakatawa da kudinshi kawai sai suka ci karo. Saurayin kuwa bai yi kasa a guiwa ba ya kira ‘yan sanda suka cafke ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel