Buhari ya yi tsokaci kan shirin janye Sojoji daga garuruwan da ake rikici

Buhari ya yi tsokaci kan shirin janye Sojoji daga garuruwan da ake rikici

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tsokaci kan yunkurin janye jami'an Sojoji daga garuruwan da aka samu sauki bayan rikice-rikice.

Buhari ya ce ba za'a janye Sojin yadda za'a jefa rayukan mazauna wurin cikin hadari ba saboda za'a janyesu ne a hankali kadan-kadan.

Zaku tuna cewa lokacin da rikice-rikicen yan bindiga suka addabi sassan Najeriya daban-daban musamman Arewa, kuma yan sanda suka gagara kawo karshensu, an baza Sojoji wuraren domin kwantar da kuran.

Yayinda yake tsokaci kan sakonni da koko-kokon baran wasu gwamnoni da sarakunan gargajiya kan shirin janye Sojojin, Buhari ya ce gwamnatinsa ba zatayi watsi da yan Najeriya dake bukatan kariya ba.

Ya yi kira ga yan Najeriya, musamman masu sharhi kan lamuran yau da kullum su yi taddaburi kan jawabin da aka saki bayan ganawarsa da hafsoshin tsaro sosai saboda an bayyana cewa sai an tabbatar da cewa komai ya koma daidai kafin sojin su janye.

Buhari Yace: "Ku kwantar da hakulanku, ba zamu sanya rayukan mutanenmu da al'ummarsu cikin hadari ba."

"Ana maganan janye Soji ne domin basu daman mayar da hankali kan aikinsu na hakika wanda shine kare kasar daga abokan gaba daga waje. Aikin yan sanda ne tabbatar da tsaro cikin gida tun da ba yaki ake a kasar ba."

"Hukumar tsaron masu farin hula NSCDC za ta taimakawa yan sanda wajen tabbatar da tsaron cikin gida idan aka janye, ba za'ayi gaggawa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel