Kalli barnar da dakarun Sojojin Najeriya suka tafka ma Boko Haram a Adamawa

Kalli barnar da dakarun Sojojin Najeriya suka tafka ma Boko Haram a Adamawa

Dakarun rundunar Sojan kasa ta Najeriya sun halaka mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram guda hudu a bata kashi da suka yi da juna a garin Michika na karamar hukumar Michika dake jahar Adamawa.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito Sojojin sun tare yan ta’addan ne a lokacin da suka yi kokarin kutsa kai cikin garin da nufin kaddamar da hare hare, inda suka mayar musu da biki, a sanadiyyar haka suka kwaci motar yaki da makamai da dama.

KU KARANTA: Tsohon shugaban NPA ya sanar da tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Kalli barnar da dakarun Sojojin Najeriya suka tafka ma Boko Haram a Adamawa

Michika
Source: Facebook

A wani labari kuma, yan Najeriya kafafaen sadarwar zamani sun bayyana bakin cikinsu gami da damuwar yadda daliban kwalejin horas da hafsoshin Sojin Najeriya, NDA, suke tare manyan hanyoyi tare da muzguna ma matafiya a duk fadin Najeriya.

Wani bidiyon dake yawo a kafafen sadarwa da jaridar The Herald ta daura ya nuna yadda daliban su biyar sanye da kayan Sojoji suka tare hanya, wanda hakan ya janyo cunkoson ababen hawa a wani babban titi.

Kalli barnar da dakarun Sojojin Najeriya suka tafka ma Boko Haram a Adamawa

Michika
Source: Facebook

Wannan lamari ya zama tamkar al’ada ne ga daliban, inda suke kiransa da Plumming 101, kuma suna yinsa ne a duk lokacin hutun Kirismeti ko sabuwar shekara. A cikin wannan bidiyo an hangi daliban suna rawa a kan titi, suna fareti, sauran kuma suna zagin matafiya dake neman a basu hanya su wuce.

Kalli barnar da dakarun Sojojin Najeriya suka tafka ma Boko Haram a Adamawa

Michika
Source: Facebook

An jiyo daya daga cikin daliban yana cewa: “Babu abin da zasu iya, Ubansu! Babu da zasu iya, dole ne su jira mu, ina take ne, ina take ne? haka nake so, zo mu tafi, wani shegen ne yake danna hon? Kai shege ne? Ubanka!”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel