Samarin da suke da mota sunfi zina da mata fiye da wanda ba su da ita - Binciken masana

Samarin da suke da mota sunfi zina da mata fiye da wanda ba su da ita - Binciken masana

- Maza matasa masu mota sun fi yin jima'i fiye da wadanda basu da ita

- Har a wannan zamanin, mata da yawa suna danganta kudin namiji ne da irin motar da yake hawa

- Hakazalika, mota an gano tana rage wa maza lokacin zuwa inda zasu tarar da matan don yin jima'in

Maza matasa masu mota sun fi yin jima'i fiye da wadanda basu da ita, bincike ya nuna.

Mallakar mota ga samari na kara musu kima kuma wannan wata alama ce da ke jan hankalin mata, masu bincike suka ce.

Masu mota suna yin jima'i a kalla sau biyu fiye da wadanda basu da ita a cikin samari, kuma basu cika amfani da kwaroron roba ba.

Mota na tallafawa matasan wajen isa inda zasu kwanta da matan kuma suna yawan amfani da ita wajen kebewa da matan.

Shugaban wannan binciken, David Soriano Hernandez yace: "tana zama tamkar wani abu dake assasa jima'i ga matasa. Har yanzu mata na nuna cewa sun fi kaunar mazan da ke da hannu da shuni ko abun duniya.

KU KARANTA: Magoya bayan Atiku ne ke son kasheni kafin zaben 2023 - Jigon PDP

"A al'adar turawa, mallakar asusun banki, gidaje da motoci duk ana dangantasu ne da kudi. Ba abun mamaki bane idan aka ce mota na jawo farin jini ga mutane ba."

Ma'abota bincike a jami'ar Mexico sun gwada tambayar maza 1,000 masu shekaru 17 zuwa 24 a kan yadda suke samun damar kwanciya da mata. Tuni suka gano rawar da mota ke takawa a wannan bangaren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel