An kori wata musulma daga wurin aiki saboda ta saka hijabi

An kori wata musulma daga wurin aiki saboda ta saka hijabi

Wata mata musulma 'yar Najeriya ta koma gida daga wajen aikinta saboda ta saka hijabi.

Folake Adebola tace, ta musulunta ne a watan Augusta kafin ta fara aiki a gidan cin abinci na Chicken Express a watan Oktoba. Watanninta uku kenan tana aiki a gidan cin abincin.

Duk da cewa a ranar Litinin din ne ta fara saka hijab zuwa wajen aiki, Adebola tace wanda ya dauketa aikin ya san cewa ita musulma ce.

"Wannan aikin na bukatar kaya na daban ne. Kuma wannan bashi daga cikin kayan aikin," cewar uban gidan Adebola a wani karamin bidiyo da ta sanya a shafinta na Twitter.

"A matsayinki na wacce nake biya, ba zan lamunci kina saka wannan ba."

Adebola mai shekaru 22 ta matukar fusatata.

DUBA WANNAN: Kano ta dara London sanyi - NIMET

"Na koma musulunci ne ba da dadewa ba kuma na fara saka hijab. Naje aiki yau amma sai ubangida na ya Kore ni saboda hijab bashi daga cikin kayan da ya kamata in saka. Yace kada in kara zuwa, ya koreni."

Ta ce, "ina shiga sai manajan yace in cire duk abinda bai shafi kayan wajen cin abincin. Nasan da hijabi na yake amma sai na koma baya, inda na cire rigar sanyi na da karamar jakata. Bayan mintoci kadan, sai ya kirani zuwa ofishinsa inda ya umarce ni da in cire hijabin don bayan cikin kayan aikina."

Rhett Warren, lauya ne dake aiki da gidan cin abincin, yace manajan bai kyauta ba da ya kori Adebola.

"Manajan da ya kori Adebola bai kyauta ba. Babu dalilin korarta don ta sakaya kanta," Warren ya ce.

Ta koma aiki a ranar Talata, bayan da mamallakin wajen cin abincin ya kirata tare da bata hakuri a kan abinda manajan yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel