Tsohon shugaban NPA ya sanar da tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Tsohon shugaban NPA ya sanar da tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Tsohon shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, Cif Bode George ya bayyana manufarsa na tsayawa takarar shugabancin kasar Najeriya a zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito duk da cewa dai Bode bai fito fili ya bayyana manufar tasa ba, amma magoya bayansa sun fara gudanar da shirye shirye tare da nema masa jama’a, mabiya da kuma masoya gabanin zaben 2023.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Ka gama rawar, za mu hadu a kotu – Magu ga Fayose

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata kungiyar siyasa mai suna Pathfinder Consortium ce kan gaba wajen jagorantar yakin neman zaben Bode, wanda ya taba zama mataimakin shugaban jam’iyyar PDP reshen kudu maso yamma.

Wani babban mashawarcin Cif Bode George, Yarima Uthman Shodipe-Dosumu ne shugaban wannan kungiyar siyasa dake jagorantar watsa manufar dan takarar. Idan za’a tuna Bode ya tsaya takarar shugabancin PDP a zaben jam’iyyar na baya, amma bai samu nasara ba.

Yan siyasa sun fara shirye shiryen siyasar 2023 tun yanzu ne sakamakon wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kare a shekarar, musamman duba da cewa Buhari ya fito ne daga yankin Arewacin Najeriya, kuma zai kwashe shekaru 8, don haka ake ganin yanzu lokaci ne na Yarbawa.

Da wannan ne ake rade radin jigon jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Bola Tinubu na daga cikin wadanda ake tunani tare da kyautata zaton zasu gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Shugaban Pathfinder, Uthman yace: “An fara babban wasa, manya suna can suna ta shirye shiryensu, tuggun siyasa ta yi nisa, kuma yan siyasa sun fara fadada tattaunawa, bamu da ra’ayin bangaranci, manufarmu shi ne dinke baraka, gyara alaka da kuma warkar da tsohon ciwo.” Inji shi.

Daga karshe Uthman yace nan bada jimawa ba zasu bayyana gwarzonsu da kara da manyan yan siyasa a zaben 2023.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel