Rayuwata na cikin hadari don naki cewa a baiwa Atiku tikitin 2023 - Shugaban dattawan PDP, Walid Jibrin

Rayuwata na cikin hadari don naki cewa a baiwa Atiku tikitin 2023 - Shugaban dattawan PDP, Walid Jibrin

Shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Walid Jibrin, ya bayyana cewa ana yi masa barazana don yaki amincewa da Atiku Abubakar kadai a matsayin dan takarar jam'iyyar a 2023

Jibrin ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba jam'iyyar za ta alanta shirin da takeyi na zaben dan takararta a 2023.

A cewarsa, dan takaran zai iya zuwa daga kowani yanki.

Yayinda yake hira da manema labarai ranar Alhamis a Kaduna, Jibrin ya ce wasu mutane sun kirashi a waya suna barazana ga rayuwarsa saboda kin amincewa a baiwa yankin Arewa maso gabas tikiti.

Ya ce sun kirashi mayaudari kuma mara kishi saboda ya ki fadin cewa Atiku Abubakar na dan takarar da akafi so.

Yace: "Na samu kira daga wasu mutane da suke yi min barazana saboda na ki cewa Arewa maso gabas za'a baiwa tikitin takarar kujeran shugaban kasa."

"Sunce ni mara kishi ne, kamata yayi in bayyanawa duniya cewa Atiku Abubakar ne dan takarar PDP daya tilo."

"Sun ce na fandare, kuma idan ban dawo kan tafarkinsu ba, zasu shirya yan bindiga su kashe ni duk inda naje."

"Sai na fadawa mutumin yaje yayi dukkan abinda yake so, shirya nike."

"Idan Inyamurai suka tambayeni, wani irin bayani zan yi musu.?"

"Ni shugaban ne, dole ne in nemi shawaran kwamitin tafiyar da lamura, gwamnoni, sannan kwamitin zantarwa ta yanke shawara. Kuma kada su manta cewa jam'iyyar nan na da kudin tsari kuma ka'ida shine wajibi a gudanar da zaben fidda gwani ga duk wanda yake son takara."

Walid Jibrin ya ce tuni ya sanar da jami'an tsaro sun kare shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel