Kisan kwamandan Iran: Zamu mayar da martani mai zafi - Ayatollah Khameini, Hassan Rouhani

Kisan kwamandan Iran: Zamu mayar da martani mai zafi - Ayatollah Khameini, Hassan Rouhani

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, ya bayyana cewa kasar Iran da abokanta za su mayar da martani kan ta'addancin Amurka na kisan kwamandan Sojin Iran kuma shugaban rundunar kwato Al-Quds, Qassem Soleimani.

Rouhani ya bayyana hakan ne da safiyar Juma'a, 3 ga watan Junairu, 2019.

Yace: "Ko shakka babu, kasar Iran da wasu kasashen yankin zasu mayar da martani kan wannan ta'addanci na Amurka."

"Kisan Soleimani da azzalumar kasar Amurka tayi ya sosa zuciyar kasar Iran da dukkan kasashen yankin."

"Kisanshi ya jaddadawa kasar Iran da sauran kasashe masu huriyya niyyar mikewa tsaye domin yakan zaluncin Amurka da kuma kare muradun addinin Musulunci."

"Wannan abin kunya ya sake bayyana raunin yankin (Larabawa)"

Bugu da kari, shugaban koli na Iran, Ayatollah Ali Khameini, ya sanar da cewa za'a kwashe kwanaki uku ana zaman makoki kuma sai an mayar da martani mai tsauri.

Mun kawo muku rahoton cewa Kasar Amurka ta kai mumunan harin jirgin sama domin hallaka babban kwamandan kasar Iran, Qassem Soleimaini da kwamandan rundunar Kata’ib Hezbollah na Iraqi, Abu Mahdi Muhandis.

Hedkwatan hukumar Sojin Amurka, Pentagon, ta tabbatar da hakan a jawabin da ta saki cewa lallai harin Amurka ya kashe kwamandan rundunar Al-Quds na Iran, Qassem Soleimani, a filin jirgin saman Baghdad dake Iraq.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel