Yadda mutane ke hijira zuwa kan duwatsu bayan harin da Boko Haram ta kai Adamawa

Yadda mutane ke hijira zuwa kan duwatsu bayan harin da Boko Haram ta kai Adamawa

Daruruwan mutane ne suka yi gudun ceton rai daga kauyukan dake da kusanci da garin Michika, dake jihar Adamawa a daren da ya gabata. Mutanen sun haye saman wani tsauni ne sakamakon harin da ake zargin na 'yan Boko Haram ne.

Harin ya auku ne wajen karfe 6 na yamma kuma ya kwashi sa'o'i masu yawa.

Wata majiya da ta zanta da jaridar Premium Times daga tsaunin Michika din tace, kauyukan Kwuapale da Kuwapa dake da kusanci da Michika ne aka hara.

Wata majiyar ta daban tace maharan sun kara gaba har zuwa kauyen Baza dake karamar hukumar Michika, lamarin da yasa mazauna yankin tserewa.

Wani mazaunin yankin Baza din ya tura wa jaridar Premium Times bidiyon mazauna kauyen suna hawa tsaunin, wasu kuma suna tafiya zuwa Yola.

DUBA WANNAN: Jiragen ruwa 18 makare da man fetur da kayan abinci suna hanyar zuwa Najeriya - NPA

Ba a gano cewa ko jami'an tsaro sun fatattaki maharan ba.

Wannan harin na Michika yazo ne a lokacin da mazauna yankin ke tsaka da bukukuwan karshen shekara. Da yawan mutanen biranen yankin sun koma kauyukansu don wadannan bukukuwan.

A lokacin da aka bada wannan rahoton, ba a samu zantawa da rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ba.

Wannan harin na Michika ya zo ne bayan kusan shekara daya da mayakan Boko Haram suka hari garuruwan dake da iyakoki inda suka kashe mutane masu tarin yawa.

Michika na da iyakoki da wasu garuruwan jihar Borno kamar su Gwoza, Askira Uba, da kuma yankunan da ta'addanci ya yawaita na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel