Shugaban kasar Amurka ne ya bada izinin kashe babban janar na Sojan Iran

Shugaban kasar Amurka ne ya bada izinin kashe babban janar na Sojan Iran

Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da daukan alhakin kisan wani babban hafsan sojan kasar Iran, Janar Qassem Soleimani a wani hari na ‘kare kai’, kamar yadda shelkwatar tsaro ta kasar, Pentagon ta bayyana.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito sanarwa daga Pentagon tace: “Bisa umarnin shugaban kasar Amurka, rundunar Sojan Amurka ta dauki matakin kare Sojojinta dake kasar waje ta hanyar kashe Qassem Soleimani.

KU KARANTA: Siyasar Kaduna: Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban karamar hukumar Zaria

“Muna da rahoton dake tabbatar da cewa Qassem yana shirya wasu hare hare da zai ma ma’aikatan jakadanci na kasar Amurka da kuma jami’an tsaron Amurka dake kasar Iraqi da yankin gabas ta tsakiya. Janar Qassem ne ya bada umarnin harin da aka kai ma ofishin jakadancin Amurka a Baghdad a makon nan.” Inji Pentagon.

Haka zalika gwamnatin kasar Amurka ta zargi Qasseem da rundunarsa ta Sojojin Quds da kashe daruruwan yan Amurka da kuma kawayenta, bugu da kari shi ne ya shirya harin roka da aka kai a ranar 27 ga watan Disamba daya kashe dan kasar Amurka guda daya.

A ranar Juma’a ne Amurka ta kashe Janar Qasseem ta hanyar amfani da wani jirgi mai sarrafa kansa daya yi masa luguden bama bamai yayin da yake cikin ayarin motoci a kan hanyarsa ta zuwa filin sauka da tasin jirage ma Baghdad.

Harin ya rutsa da Qasseem da mataimakin shugaban Sojojin yan shia na Hashd Shaabi, Abu Mahdi Al-Mohandes da wasu manyan Sojojin kasar Iran guda 25. Haka zalika jim kadan bayan wannan hari, Sojojin Amurka sun kashe Mohammed Reda Al-Jaberi, mai magana da yawun Sojojin Shia da jami’ansa 5.

Jami’an rundunar Sojan Iraq sun tabbatar da kisan Qasseem, inda suka ce sun hangi saukar rokokin bamabamai guda uku a kan wasu ayarin motoci guda biyu, wanda suka kashe mutane da dama dake yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng