Gwamnatin jihar Zamfara ta ware N7bn don gina sabon gidan gwamnati

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware N7bn don gina sabon gidan gwamnati

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira bilyan bakwai a kasafin kudin 2020 domin gina sabon gidan gwamnati, a cewar sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bala Bello.

Bello ya bayyana hakan ne ranar Alhamis ne yayinda yake kare muradun ofishinsa a majalisar dokokin jiha.

Bello ya ce gwamnatin jihar ta yanke shawaran gina sabuwar gidan gwamnati saboda bukatar hakan.

Yace: "Kun san gidan gwamnatin dake karamar hukumar Gusau tun zamanin tsohuwar jihar Sokoto. An yi amfani da ita ne na wucin gadi lokacin da aka kirkiro jihar a 1996"

"Muna bukatar sabuwar gidan gwamnatin zamani domin shiga sahun sauran jihohi."

"Idan aka kammala gina ta, za'a mayar da tsohuwar gidan gwamnatin sakatariya."

Bugu da kari, Gwamnatin jihar Zamfara ta ware makuden kudi har naira biliyan daya don gina masallatai da kuma gyara makabartu.

Gwamnatin jihar ce ta tabbatar da ware wannan kudin don gina masallatan Juma'a, gyaran makabartu, kayan azumi da sauran lamurran addini a jihar a shekarar 2020.

Kamar yadda rahoton jaridar Independent Nigeria ta ruwaito, kwamishinan al'amuran addinin musulunci na jihar, Sheikh Tukur Jangebe ya bayyana hakan ne yayin kare kasafin kudin ma'aikatarshi a gaban majalisar jihar a Gusau a ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel